Yajin Aiki: kungiyoyin SSANU da NASU Sun nuna rashin gamsuwa da rahoton Kwamitin da Nimi Briggs ya mikawa gwamnatin tarayya

SSANU NASU
SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandire sun nuna rashin gamsuwa da rahoton kwamitin da Farfesa Nimi Briggs ya mika wa gwamnatin tarayya domin amincewa da shi.

Kungiyoyin sun hada da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’I ta kasa (wato SSANU) da kuma kungiyar ma’aikatan ilimi da hadin kai (wato NASU).

Shugaban kwamitin hadin gwiwar wato JAC, Mista Peters Adeyemi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasa NAN ya ruwaito cewa SSANU da NASU sun shiga yajin aiki na tsawon watanni hudu saboda rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da kungiyoyin.

A cewarsa, abin mamaki ne a ce ko kadan ba mu fara tattaunawa kan batun tantance albashi da sauran alawus-alawus ba.

“Mun samu rahoton cewa kwamitin ya riga ya gabatar da rahoto ga Gwamnatin Tarayya inda ya ba da shawarar karin kashi 10 ga kungiyoyin da ba na koyarwa ba.

“Mun gano cewa akwai lam’a a kwamitin ya zuwa yanzu, mun tabbatar da komai” in ji shi.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

Ya ce bayan taron farko, kungiyoyin biyu – NASU da SSANU sun tilasta wa kansu da kansu su haifar da tunanin cewa kwamitin ba shi da cikakken bayanin ayyukansa.

Shugaban JAC ya bayyana cewa tarurrukan biyu da aka yi da kwamitin Briggs da kungiyoyin, ba a tattauna batun karin albashi da alawus-alawus ba.

“Yayin da kungiyoyin NASU da SSANU suka gabatar da takardar bukatu da suka hada da shawarwarin duba albashi tare da tsara jadawalin albashin yadda ya dace.

“Kwamitin ya roki kungiyoyin biyu su dauki batun duba albashi da alawus-alawus a karshe.

Don haka ya ce ya kamata a bayyana karara cewa kungiyoyin SSANU da NASU sun yi watsi da duk wata shawarar albashi da za ta kara haifar da baraka a tsarin jami’o’in.

Sai dai ya bukaci hukumar NITDA da ta hanzarta aiwatar da aiki tare da fitar da sakamakon bincikenta domin a huta da cecekucen da ake tafkawa na tsarin biyan albashi mai inganci kuma mai dorewa wanda ya dace da tsarin Jami’o’in Najeriya,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa ba burin NASU da SSANU ba ne su durkusar da tsarin amma an tilasta su ne saboda rashin kulawa da tsarin jami’o’in.

Ya kara da cewa, ya zuwa yau, cikin batutuwa takwas da suka jawo yajin aikin, babu daya daga cikinsu da gwamnati ta yi magana a kai.

“Ba a biya mafi karancin albashin ma’aikata ba, kamar yadda a yawancin jami’o’i, har yanzu muna da mambobi da yawa da ba a biya su ba,” in ji shi.


Ya kuma yabawa kungiyar Kwadago ta Najeriya bisa irin gudunmawar da ta yi wajen ganin an shawo kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here