Nan ba da jimawa ba Yan Najeriya zasu San halin da PDP ke ciki-Wike

892D5D4E C42D 4B96 B81F EF5E6F3669FD
892D5D4E C42D 4B96 B81F EF5E6F3669FD

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi alkawarin bayyana abubuwan da ke faruwa, na baya-bayan nan a jam’iyyar PDP.

Ana kyautata zaton Wike ya fusata ne kan matakin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, na daukar gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda zai masa mataimaki a takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Arise a kwanakin baya, Atiku ya bayyana dalilin da yasa bai zabi Wike a matsayin abokin takarar sa ba duk da shawarar da aka ce kwamitin da PDP ta kafa, ta bayar.

Wike dai ya ci gaba da tada kura a jam’iyyar tun bayan faruwar lamarin inda rahotanni da dama ke nuni da cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar ta PDP.

Ko a ranar asabar 23 ga watan Yulin shekarar da muke ciki ta 2022 ma a shafinsa na Twitter Wike, ya bayyana cewa zai magantu nan ba da jimawa ba kan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar
A baya dai an ruwaito cewa tawagar gwamnonin jam’iyyar APC sun ziyarci Wike a gidansa da ke Fatakwal, lamarin da ya haifar da wani sabon rade-radin sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Kafin hakan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi tattaki zuwa jihar Rivers inda ya gana da gwamna Wike.

Duk da cewa babu wasu cikakkun bayanai game da ganawar ta Wike gwamnonin APCin da kuma Peter din ba, ana dai ci gaba da yin hasashe ne game da yiwuwar Wike ya fice daga PDP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here