Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya sababbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar murna.
Murtala Garo a cikin sakon taya murnar da ya fitar a yau Lahadi ya ce, babban taron da aka gudanar a jihar Kano ya nuna yadda jam’iyyar ke mu’amala da mambobinta.
Haka kuma ya ce, matuƙar Abdullahi Abbas ya cigaba da jagorancin jam’iyyar kamar yadda ta samu nasara a babban zaben 2019, to tabbas zai maimaita irin wannan nasara a babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.
Kwamishinan ya yaba da salon jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda ke bai wa dukkan mambobin jam’iyyar dama dai-dai kuma yana ba da goyon bayan jagoranci ga kowa da kowa.
” Muna matukar godiya da goyon bayan gwamnan a kowane lokaci da kuma ci gaban da yake samu, ” in ji sanarwar.
Haka kuma ya buƙaci sabon shugaban APC Abdullahi Abbas da ya yi koyi da kyawawan halayen gwamna Abdullahi Ganduje ta hanyar haɗa kan dukkan mambobin jam’iyyar tare da ɗinke ɓarakar da ke cikinta.













































