Mahaifiyar fitaccen dan kasuwar jihar Katsina, Dahiru Mangal ta rasu.
Hajiya Murja Mangal ta rasu ne a daren Alhamis bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
A cewar majiyoyi, tana da shekaru 85.
Majiyar ta ce za a yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan sallar Juma’a da karfe 3:00 na rana a yau.
Solacebase ta ruwaito cewa ta bar ‘ya’ya hudu da suka hada da Alhaji Dahiru, Alhaji Bashir, Hajiya Hauwa da kuma Hajiya Zulai.
Majiyar ta ce za a rika tunawa da ita sosai saboda ayyukan taimakon al’umma da ta yi, da kuma daruruwan mutanen da take ciyar da su kullum a Katsina.
Alhaji Dahiru Barau Mangal shi ne shugaba, kuma babban jami’in kamfanin Afdin Group of companies Nigeria Limited, Max Air Limited, Katsina Dyeing and Printing Textiles Limited.













































