An kama daya daga cikin manyan masu fataucin miyagun kwayoyi a cikin jerin sunayen ‘yan sandan Interpol, dan Najeriya, Chukwu Ogbonna David wanda aka fi sani da Tony, a Hyderabad, babban birnin jihar Telangana ta kudancin Indiya.
An kama mutumin mai shekaru 37 a ranar Alhamis tare da wasu masu amfani da muggan kwayoyi guda tara a Hyderabad a wasu wurare daban-daban.
‘Yan sandan sun kuma gano Tony ya kafa wata hanyar sadarwa ta wakilai a wurare daban-daban da suka hada da Mumbai, Goa da Hyderabad, inda yake karbar kudade ta yanar gizo, sannan kaiwa mutane kwayoyin.
“Tony ya gudanar da ayyukansa galibi a jihohin Kudancin Indiya. Har ila yau, muna binciken ko masu siyayyar sun kasance suna yin liyafa kuma suna amfani da miyagun ƙwayoyi, “in ji ‘yan sanda.
An kama Tony daga Mumbai, kuma bisa ga bayanin da ya bayar, an kama wasu masu saye da sayar da kayayyaki 9, galibi ’yan kasuwa, tare da kwace gram 10 na hodar iblis.
Kwamishinan ‘yan sanda na Hyderabad CV Anand ya tabbatar da cewa Tony yana siyan miyagun kwayoyi daga wani mai safarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa, Star Boy, dan Afirka, ta jiragen ruwa.
Sauran mutane bakwai da aka kama ‘yan kasuwa ne, an bayyana sunayensu da; Niranjan Kumar Jain, Shashwat Jain, Yagyanand Agarwal, Dhandul Surya Sumanth Reddy, Bandi Bhargav, Venkat Chalsani and Thamminedi Sagar.
Jaridar Siasat Daily ta ruwaito cewa Tony, wanda ya yi hijira zuwa Mumbai daga Najeriya a 2013 a kan takardar VISA na wucin gadi, kuma ya zauna a Mumbai ba bisa ka’ida ba tun lokacin, ya yanke shawarar shiga kasuwancin miyagun ƙwayoyi 2017 kuma ya kulla hulɗa da masu amfani da su a Mumbai, Goa da Hyderabad.













































