Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tawagar shugabanin APC, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje a dakin taro dake fadar shugaban kasar dake Abuja.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana makasudin taron ba, an tattaro cewa mahalarta taron za su gabatar da takarda mai dauke da muhimman shawarwari kan dakile rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar.
Wata majiya ta ce taron da aka fara da misalin karfe 3:00 na agogon kasar yana bukatar halartar hafsoshin tsaro saboda yana iyaka da tsaron kasa.












































