Cire Tallafin Mai: Shugabannin Kwadago sun caccaki Shugaban Majalisar Dattawa

0F4A9853 70B3 4EC9 930B 987C019362E5
0F4A9853 70B3 4EC9 930B 987C019362E5

Shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC sun soki kalaman shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da masaniya kan wani shiri na janye tallafin man fetur a kasar.

Solacebase ta ruwaito a ranar Talata cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban ya bayyana cewa bai bada umarnin cire tallafin man fetur ba.

‘yan kwadagon da suka dage cewa babu yadda za a yi shugaba Buhari ya yi ikirarin rashin sanin matakin cire tallafin, sai dai sun bukaci shugaban majalisar dattawan da ya daina haifar da rudani a kasar.

Shugabannin kwadagon wadanda suka bayyana hakan a jiya yayin taron kungiyar NLC na jihar Kano sun bayyana cewa ma’aikata ba za su amince da duk wata dabarar da gwamnati za ta yi na janye tallafin man fetur da kuma karin farashin famfo ba.

Tsohon Mataimakin Shugaban NLC, Kwamared Isa Tijani  ya ce Ministan Kudi da kuma Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ba su iya yadda ba, ba tare da amincewar Shugaba Buhari ba.

Kwamared Isa ya kuma kalubalanci shugaban kasar da ya fito fili ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya kan matakin da gwamnati ta dauka kan tallafin man fetur, wanda shugaban kungiyar kwadagon ya ce shi ne kadai maganin da zai haifar da shakku da hasashe.

“Yaya shugaban kasa zai ce bai san da maganar cire tallafin man fetur, a lokacin shugaban NNPC ya tabbatar, ita ma ministan kudi ta tabbatar da shirin, sai kawai ya ce bai sani ba. Shin wadannan manyan jami’an gwamnati suna aiki ne a madadinsa ko kuma sun sabawa umarninsa? Shin za su sami damar yin wani abu ba tare da saninsa ba, shin hakan zai yiwu?

“Kada Shugaban Majalisar Dattawa ya zo ya kara ruda ‘yan Najeriya domin ba za mu yadda da duk wani yunkuri na janye tallafin ba. Kuma a kowane hali, me yasa shugaban kasa ba zai fito da kansa ya sanar da cewa gwamnati ba kuma ba za ta cire tallafin ba. Idan maganar ta fito daga shugaban kasa a matsayin C a C, zai dauka amma duk wani mutum, ba amsa ba ce.

A nasa bangaren, tsohon babban sakataren kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Salisu Mohammad ya caccaki gwamnati kan kashe biliyoyin naira da sunan kula da matatun mai ba tare da sakamako ba, ya kalubalanci shugaba Buhari da ya cika alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe na dakile cin hanci da rashawa a kasar nan.

Kwamared Salisu ya bayyana cewa maimakon a gyara matatun man da ake amfani da su don saukaka farashin man da ake amfani da su a cikin gida, gwamnati mai ci ta kashe biliyoyin daloli wajen shigo da mai tare da karfafa gwiwar masu cin hanci da rashawa su rika satar dukiyar kasa da sunan tallafi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here