Majalisar Dokokin Kano Ta Gayyaci Shugaban Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Na Jihar

kano assembly new e1631549518816
kano assembly new e1631549518816
Majalisar dokokin jihar Kano ta gayyaci shugaban hukumar tara kudaden shiga na jihar Abdulrazak Datti Salihi da ya bayyana a gabanta kan ayyukan hukumar.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdul Madari, mamba mai wakiltar mazabar Warawa ne ya gabatar da kudurin yayin zaman majalisar na ranar Litinin.
Bayanan da jaridar Solacebase ta samu shine kudurin ya samu goyon bayan mataimakin shugaban masu rinjaye, Abdullahi Iliyasu Yaryasa, mamba mai wakiltar mazabar Tudun Wada.
Daga nan Majalisar ta amince da bukatar inda Kakakinta, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya sanar da gayyatar Shugaban a gaban majalisar gobe 14 ga Satumba 2021.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Uba Abdullahi ya fitar ta ce majalisar ta kuma samu wasikar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin tantancewa da tabbatar da nadin mambobin Hukumar kula da  ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Kano kamar yadda yake a kundin doka karkashin sashi na huɗu sakin layi na ɗaya.
A cewar sanarwar, mambobin sune: Nasiru Mu’azu Kiru daga Karamar Hukumar Kiru, a matsayin Shugaba dakuma Ishaq Tanko Gambaga daga Karamar Hukumar, Hon Ali Abdu daga Karamar Hukumar Doguwa, Salisu Abubakar daga Karamar Hukumar Makoda, Isyaku Umar Rurum daga Karamar Hukumar Rano, Ladan Sabo Ahmad daga Karamar Hukumar Sumaila, Gambo Ibrahim Mai Wada daga Karamar Hukumar Makoda, Ukashatu Bello daga Karamar Hukumar Dambatta, Naziru Zakari Sheka daga Karamar Hukumar Kumbotso da Sule Musa Adnan daga Karamar Hukumar Warawa a matsayin Membobi.
An umarci Kwamitin Majalisar dake kula da fannin da su gudanar da aikin tantancewa don tabbatarwa.
Majalisar ta mika aikin ga Kwamitin kula da kudade na Majalisar don ci gaba da gudanar da aikin kuma an ba shi watanni uku da ya gabatar da rahoton sa ga majalisar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here