EFCC ta gurfanar da wata mata a Kano bisa zargin almundahanar naira miliyan N32

395A97BD 04F2 4592 A52F 564F37FBC229
395A97BD 04F2 4592 A52F 564F37FBC229

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a ranar Alhamis, ta gurfanar da wata Wasila Musa Ibrahim da kamfaninta mai suna Najaatu Petroleum Limited a gaban mai shari’a Mohammed Nasir Yunusa a babbar kotun tarayya dake Kano.

Solacebase ta bayar da rahoton cewa an gurfanar da ita a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 10 da suka shafi halasta kudaden haram da kuma kaucewa biyan haraji.

Wanda ya shigar da karar ya yi zargin cewa a wani lokaci a shekarar 2020 wadda ake kara ta tunkare shi da wata takarda ta kasuwanci don samar da man Diesel da Premium Motor Spirit (man fetur) ga wani kamfani mai suna Lee Group.

A cewar EFCC, wadda ake zargin ta karbi kudi har miliyan Talatin da Takwas da Naira Dubu Dari Biyu (N38, 200,000.00) daga hannun wanda ya shigar da karar tare da iyalansa domin gudanar da kasuwancin amma ta karkatar da kudin don amfanin kanta.

Lokacin da mai karar ta bukaci a mayar  da kudin, wadda ake kara ta ce ta bayar da kudin ne ga wani Alhaji Lawan da ya arce amma ba a same shi ba.

A yayin gudanar da bincike, an gano cewa, babu wata shaida da ta nuna cewa wadda ake tuhuma ta saka kudin da aka fada.

An kuma gano cewa kamfaninta na Najaatu Petroleum Limited ya kaucewa biyan haraji daga watan Janairun 2013 zuwa 2020.

Wadda ake tuhumar ba ta amsa laifin ba.

Lauyan masu shigar da kara, Y.J Matiyak, ya roki kotun da ta sanya ranar sauraron karar tare da tasa keyar wadda ake kara zuwa ga  EFCC.

Sai dai lauyan wadda da ake kara, Suleiman Abdulrahim ya sanar da kotun bukatar neman belin wadda ake kara, sannan ya bukaci a shigar da wanda yake karewa beli.

Mai shari’a Yunusa, bayan ya saurari lauyoyin masu kara, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairun 2022 domin sauraren neman beli, sannan ya tasa keyar wanda ake kara a hannun EFCC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here