SERAP ta bukaci kotu ta dakatar da shirin shugaba Buhari na bibiyar sakonnin yan Najeriya

SERAP Buhari
SERAP Buhari

Kungiyar SERAP mai rajin tabbatar da adalci a ayyukan ‘yan majalisu, ta shigar da kara kan shirin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, na bibiyar sakonni da kuma tattaunawar da ‘yan Najeriya ke yi a manhajar WhatsApp, inda ta nemi kotu ta bayyana shirin da gwamnatin ke niyyar yi a matsayin abinda yake ba bisa ka’ida ba, tare da keta haƙƙin adana sirri.

Shigar da Karar ya biyo bayan tanadin da ke cikin dokar kasafin Kudin da aka sanya hannu a watan Yulin bana 2021 don kashe Naira biliyan 4 da miliyan 87 don sa ido kan kira da sakonni.

Adadin kudin na daga cikin karin kasafin kudi na Naira biliyan 895 da miliyan 8 da majalisar dokoki ta amince da shi.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1240/2021 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman: “umarnin har abada na hana shugaba Buhari da duk wata hukuma, ko gungun mutane daga sa ido ba bisa ka’ida ba akan saƙonnin WhatsApp, kiran waya da saƙon rubutu na ‘yan Najeriya da sauran mutane.”

Haka kuma SERAP ta kuma bukaci “sanarwar cewa duk wani sa ido kan sakonnin WhatsApp, kiran waya da sakonnin rubutu zalunci ne kuma abin tsoro ne, saboda yana yin barazana kuma ya saba wa sashe na 37 da 39 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yiwa kwaskwarima da mataki na 9 na Yarjejeniyar Afirka kan hakkokin dan adam da Jama’a.

SERAP ta kuma bayyana adawarta da cewa, “Shirin sanya ido kan sakonnin WhatsApp, kiran waya da sakonnin rubutu tsoma bakin gwamnati ne ba tare da wani dalili ba dangane da rayuwar iyali da ta masu zaman kansu.

A cewar SERAP, “Gwamnatin Buhari tana da nauyin da ya rataya a wuyanta na kare ‘yan Najeriya da sauran mutane daga katsalandan ba bisa ka’ida ba da take hakkokin su, Kula da saƙonnin WhatsApp da kiran waya da saƙonnin rubutu zai ba hukumomin gwamnati damar sanya ido kan gudanar da sa ido kan hanyoyin sadarwa na mutane.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here