Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya umarci sabbin membobin kwamitin zartarwar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kwara da su yi aiki tukuru don kwato mulkin jihar.
Saraki ya bayyana hakan ne a karshen makonnan a birnin Ilorin a karshen babban taron jam’iyyar bayan tabbatarda wadanda suka samu nasara.
Ya ce, “Ya kamata ku fara aiki da himma don tabbatar da nasarar jam’iyyar gaba daya a babban zaben 2023.”
“Da zaran kun bar wannan wurin, ya kamata ku fara aiki, Halin zaman lumana na wannan babban taron ya tabbatar min da cewa a shirye muke mu dawo da mulki a Kwara,” in ji shi.
Tsohon shugaban majalisar dokokin Kwara, Alhaji Mohammed Babatunde, ya zama shugaban jam’iyyar, yayin da Umaru Muhammed ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar.
Tunde Ashaolu ya rike mukamin Sakataren yada Labarai a karshen taron.
Sauran wadanda suka zama jagororin jam’iyyar sakamakon yin sulhu sun hadar da Bisi Fakayode, da Baba Jimoh, Shugaban Yankin Sanatan Arewa da Haliru Dansoho, a matsayin Shugaban Matasa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar sun yi aiki ta karkashin kasa don amincewa da tsarin yarjejeniya.
A jawabinsa na godiya, sabon shugaban, Babatunde ya ce, bai san aikin da ke gabansa ba, ya kara da cewa ya shirya domin tunkarar aikin.
Ya ce, “Za mu fara aiki tun daga tushe kuma za mu tabbatar da cewa mun samu nasara.
“Za mu yi amfani da zabukan kananan hukumomi na gaba don nuna wa mutanen Kwara cewa mun dawo, ” in ji shi.
Hon John Akwarashi, shugaban kwamitin zaben daga shalkwatar jam’iyyar PDP ta kasa da ke birnin tarayya Abuja, cewa ya yi abun farin ciki ne a tabbatar cewa al’ummar Kwara sun cigaba da amincewa PDP.
“A bayyane yake cewa zabin jami’ai shi ne zabin mafi yawan mambobin jam’iyyar,” in ji shi.
Jami’in da ya jagoranci tawagar INEC zuwa babban taron, Malam Shehu Abdulkadir, ya ce, “Daga abin da muka gani, a bayyane yake cewa zabin yarjejeniya shi ne babban zabin mambobin jam’iyyar”.
Mahalarta taron sun hada da tsohon Gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed, da tsohon Ministan wasanni Bolaji Abdullahi da Abubakar Kanike tsohon dan majalisar wakilai.
NAN













































