Jam’iyyar PDP ta zabi Yusuf Ado Kibiya a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a Kano
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban kwamitin zaben daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa Halilu Abubakar Mazagani ne ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi.
Kibiya ya samu gagarumin rinjaye inda ya samu kuri’u 3,964 inda ya doke abokin hamayyarsa Nura Nuhu wanda ya samu kuri’u 244.
Bayan sanarwar, Barista Abdul Fatah Muhammad ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar na jihohi 39 da suka hada da Hon. Kibiya.
Ana sa ran sabon shugabancin zai tafiyar da al’amuran jam’iyyar PDP a Kano, yayin da jam’iyyar ke kokarin kara karfin ta da dabarun tunkarar harkokin siyasa masu zuwa.
A jawabinsa na karramawa, Hon. Kibiya ya godewa ‘ya’yan jam’iyyar bisa amincewar da suka yi masa, ya kuma yi alkawarin yin shugabanci cikin gaskiya da rikon amana, da nufin farfado da jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Kibiya ya taba rike mukamin kwamishinan noma a zamanin Sanata Rabiu Kwankwaso tsakanin 1999-2003.












































