Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke shi, yana mai cewa shi da kansa ya je ofishin hukumar domin wanke sunansa kan wasu korafe-korafe marasa tushe da shigar akansa.
Kwankwaso ya ce, ya ziyarci shalkwatar hukumar jiya Asabar don bata bayanai dangane da zargin, inda ya gana da jami’an hukumar ta EFCC na wasu sa’o’i.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar a yau Lahadi tare da aike wa jaridar Solacebase.
A baya dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a watan Satumba kan zarginsa da aikata almundaha, karkatar da dukiyar al’umma da kuma karkatar da kadarorin gwamnati ga wasu mukarraban gwamnatinsa amma ya kasa amsa gayyatar.
Sai dai an yi wa tsohon gwamnan na jihar Kano tambayoyi na awanni da dama jiya Asabar wanda aka yada a kafafen yada labarai, duk da cewa tsohon Ministan tsaron ya musanta kama shin amma dai ya kai kansa hukumar.
Ana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kudaden ‘yan fansho da ya kai naira biliyan 10 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, don samar da aikin ginin gidaje ga abokansa, kamar yadda zargin hukumar ta EFCC ya bayyana.
Haka kuma Solacebase ta ruwaito cewa Sanata Kwankwaso ya bayyana tuhume-tuhumen hukumar a matsayin cewa, ta bayyana karara siyasa kawai da wasu abokan hamayyarsa suka hada kai da nufin kunyata shi, yana mai cewa babu gaskiya a kan dukkan zargin.
“Jita-jitar kama ni karya ce kuma mara tushe, a matsayina na mai bin doka da mutunta ta, ni da kaina na ziyarci hukumar a ranar Asabar domin in share sunana kuma abin da ya faru ke nan ”.
“Na gana da su, jami’an EFCC na shaida musu cewa na zo ne don wanke sunana a kan takardar da aka rubuta tun 2015 kan ni, na ba da amsoshin duk tambayoyin da jami’an suka yi.” in ji tsohon gwamnan.













































