Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya koma APC

Anambra Dep Gov1
Anambra Dep Gov1

Mataimakin gwamnan jihar Anambra Nkem Okeke ya sauya sheka daga jam’iyar APGA zuwa APC mai mulki a Najeri.

An gabatar da Mr Okeke ga Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba, ta hanyar Shugaban jam’iyar na riko kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da kuma gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Gwamna Uzodinma, wanda ya gabatar da sabon dan jam’iyyar APC ga shugaban kasa, ya yi wa manema labarai na fadar gwamnati karin haske a karshen taron.

Ya ce yana da kwarin gwiwa cewa za a samu karin sauye -sauyen sheka zuwa jam’iyya mai mulki kafin zaben gwamna na ranar 6 ga Nuwamba da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar a jihar Anambra.

Gwamnan, duk da haka, ya musanta zargin da Gwamna Willi Obiano na Anambra ya yi na cewa ‘yan majalisar dokokin jihar da suka sauya sheka daga jam’iyyar APGA sun samu wasu kuɗaɗe saboda shiga jam’iyyar.

Ya jaddada cewa a maimakon jan hankalin ‘yan majalisar da kudi, an yi musu liyafa ta hanyar lallashi da ba da shawara ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here