Yadda na taimaka wa Tinubu ya lashe zaɓen 2023 – Lai Mohammed

lai mohammed new

Tsohon ministan yaɗa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana irin dabarun yaƙin neman zaɓe guda biyu da ya yi amfani da su, waɗanda suka taimaka wa jam’iyyar APC da Bola Tinubu wajen samun nasara a zaɓen shekarar 2023.

Lai Mohammed ya yi wannan bayani ne a cikin littafinsa da aka ƙaddamar kwanan nan mai taken Headlines and Soundbites: Media Moments that Defined an Administration, inda ya rubuta abubuwan da suka faru a lokacin da yake aiki a ƙarƙashin marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ya tunatar da cewa gabanin zaɓen 2023, Muhammadu Buhari ya gargadi ministoci da manyan jami’an gwamnati da kada su bar ayyukansu na hukuma domin shiga harkokin yaƙin neman zaɓe, tare da jan hankalin cewa duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci hukunci.

Sai dai Lai Mohammed ya bayyana cewa, ba tare da karya umarnin shugaban ƙasa ba, ya aiwatar da dabarun yaƙin neman zaɓe ta hanyar kare gaskiya, rubuta nasarorin gwamnati, da tabbatar da cewa ba a sauya tarihin ayyukan gwamnati ta hanyar farfaganda ba.

Ya bayyana cewa a wancan lokaci, ra’ayin da ke yawo a ɓangaren jam’iyyun adawa shi ne gwamnatin APC ƙarƙashin Muhammadu Buhari ba ta cimma wani abin a zo a gani ba, don haka babu dalilin dawo da jam’iyyar kan mulki.

Karanta: Yadda wani minista ya raina ni a taron majalisar zartarwa ta ƙasa – Lai Mohammed

A cewarsa, wannan ikirari ba gaskiya ba ne, illa wani shiri na ɓata suna da nufin raunana APC da Bola Tinubu kafin zaɓe.

Lai Mohammed ya ce domin tinkarar wannan yanayi, ma’aikatarsa ta ƙaddamar da shirin PMB Administration Scorecard Series, wanda ya gabatar da cikakkun bayanai kan nasarorin gwamnatin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023, inda ministoci suka gabatar da hujjoji da bayanai na ainihi game da ayyukan da aka aiwatar a sassan da suke kula da su.

Ya ƙara da cewa an yi amfani da dabarun sadarwa na zamani da na gargajiya domin isar da sakon ga jama’a, sannan aka ƙaddamar da wasu kayayyakin adana tarihi kamar faifan bidiyo, tarin shaidu, kundin nasarorin gwamnati da kuma wani dandali na intanet da ke bai wa mutane damar samun bayanan daga ko’ina a duniya.

A ƙarshe, Lai Mohammed ya bayyana cewa wannan tsari ya tilasta jam’iyyun adawa shiga yanayin kare kai, tare da karya labaran ƙarya da ake yadawa kan gazawar gwamnati, sai dai amfani da hujjoji da bayanai masu tabbaci ya taimaka wajen jan hankalin masu jefa ƙuri’a da ba su yanke shawara ba, tare da tabbatar da muhimmancin dabarun sadarwa wajen tasiri kan sakamakon zaɓe.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here