Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar malamai ta jami’o’i ASUU inda ta bayyana ta a matsayin muhimmin mataki na dawo da daidaito, amincewa da inganci a tsarin ilimin manyan makarantu na Nijeriya.
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a lokacin gabatar da yarjejeniyar a Abuja, tare da cewa matakin ya nuna ƙudurin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na tabbatar da ilimi mai sauƙin samu, mai inganci da kuma kalandar karatu ba tare da tangarda ba.
Ministan ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya ɗauki alhakin warware tsoffin rikice-rikicen da suka shafi jami’o’i tsawon shekaru, ta hanyar fifita tattaunawa da gyara maimakon jinkiri, domin tabbatar da zaman lafiya a tsarin ilimi.
A cewarsa, muhimmin tanadi a cikin yarjejeniyar shi ne duba albashin malamai a manyan makarantu na tarayya, bisa amincewar hukumar albashi ta ƙasa, wanda zai fara aiki daga ranar farko ta shekarar 2026, inda aka ƙara albashin malamai da kashi 40 domin ƙara ƙwarin gwiwa da rage ƙauracewar ƙwararru zuwa ƙasashen waje.
Karanta: Yadda na taimaka wa Tinubu ya lashe zaɓen 2023 – Lai Mohammed
Ya ƙara da cewa wannan ƙarin albashi ya haɗa da wani alawus na kayan aikin ilimi da aka haɗa cikin albashi, wanda zai rufe wallafa mujallu, halartar tarurrukan ilimi, amfani da internet, kuɗin membobinsu na ƙungiyoyin ilimi da sayen littattafai, tare da sake tsara wasu alawus-alawus na ilimi domin ƙara gaskiya da adalci.
Ministan ya kuma sanar da ƙirƙiro sabon alawus na musamman ga farfesoshi da manyan malamai, inda farfesoshi za su riƙa karɓar ƙarin kuɗi na shekara-shekara, haka kuma manyan malamai, domin tallafa musu wajen bincike, koyarwa da jagoranci a fannin ilimi.
Shugaban ƙungiyar malamai ta jami’o’i, Farfesa Chris Pinuwa, ya bayyana cewa yarjejeniyar ta 2025 ta samo asali ne daga dogon tsarin tattaunawa da aka fara tun 2017.
Ya kuma yaba wa gwamnati da kwamitin tattaunawar kan kammala yarjejeniyar, tare da jaddada cewa har yanzu akwai batun ‘yancin kai na jami’o’i da ke buƙatar ƙarin kulawa domin bunƙasa ilimin ƙasa.
NAN













































