Gwamnatin Jihar Niger ta bayar da wa’adin watanni biyu ga mutanen da ke zaune a ƙananan ƙauyuka da ke kewaye da Tafkin Kainji domin su fice daga yankin, inda Majalisar Masarautar Borgu za ta sake tsugunar da su a wasu wurare da suka dace.
Wannan umarni ya fito ne ta cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai ga gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, ya fitar, inda ya bayyana cewa gwamna Muhammad Umar Bago ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya fadar Sarkin Borgu da ke sabuwar Bussa.
A yayin ziyarar, gwamnan ya jajanta wa Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad-Haliru Dantoro, Kitoro na huɗu, da al’ummar masarautar baki ɗaya bisa harin ta’addanci na baya-bayan nan da ya yi sanadin rasa rayuka masu yawa.
Gwamnan ya bayyana cewa sake tsugunar da mutanen ya zama wajibi domin kauce wa hasarar da ba a yi tsammani ba, ganin cewa gwamnatinsa tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya sun kuduri aniyar share dazukan yankin domin kawar da masu laifi da ke amfani da Tafkin Kainji a matsayin sansani, lamarin da ya sa yankin ya zama abin fargaba ga mazauna yankin.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yawaitar shigowar mutane cikin masarautun ba tare da tantancewa ba, wanda hakan ya zama barazana ga tsaro, yayin da ayyukan masu ba da bayanan sirri ke hana ƙoƙarin jami’an tsaro cimma nasara a yankin.
Gwamnan ya bukaci Majalisar Masarautar Borgu da ta tashi tsaye ta haɗa ƙarfi da jami’an tsaro da gwamnatoci a dukkan matakai domin yaƙi da duk wani nau’in rashin tsaro a masarautar, tare da sake jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, yana mai roƙon Allah Ya jikan su.
A nasa ɓangaren, ƙaramin ministan noma da tsaron abinci, Dakta Aliyu Abdullahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na da sha’awar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar, yana mai nuna muhimmancin ɗaukar matakai na zahiri wajen ƙaura da mutanen kafin a karɓe dazukan domin amfanin al’umma.
Sarkin Borgu ya yi alƙawarin yin aiki tare da hukumomi domin gano da gurfanar da masu ba da bayanan sirri.
NAN













































