Duk da manufar “babu aiki babu albashi”: JOHESU ta dage kan ci gaba da yajin aiki

JOHESU (1)

Haɗakar ƙungiyar Ma’aikatan Sashen Kiwon Lafiya ta Haɗin Gwiwa da Majalisar Ƙwararrun Masu Aikin Kiwon Lafiya, JOHESU, ta jaddada aniyarta na ci gaba da yajin aiki a ƙasa baki ɗaya na dindindin, duk da aiwatar da manufar “babu aiki babu albashi” da gwamnatin tarayya ta sanar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na ƙasa, Martin Egbanubi, ya sanya wa hannu, wadda aka aikawa shugabanni, manyan sakatarori da shugabannin jihohi na ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin JOHESU, a ranar Talata a Abuja.

JOHESU ta bayyana cewa wannan matsaya ta biyo bayan kudurorin da shugabancin ƙungiyar na ƙasa ya cimma a wani taron gaggawa da aka gudanar a internet ranar 12 ga watan Janairu, domin nazari kan abubuwan da suka shafi yajin aikin.

Ƙungiyar ta tunatar da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin aiwatar da manufar “babu aiki babu albashi”, tare da dakatar da albashin mambobinta ta hannun ofishin Akanta Janar na Tarayya.

JOHESU ta ce yajin aikin ya samo asali ne daga daɗaɗɗiyar buƙatarta na aiwatar da tsarin albashi na CONHESS da aka gyara, tare da sauran buƙatun jin daɗin ma’aikata.

Karanta: JOHESU ta soki matakin garambawul na shekarun ritaya da gwamnatin tarayya ta yi a ɓangaren lafiya

Ƙungiyar ta ƙara da cewa shugabancin ta na ƙasa ya duba rahotanni daga ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da kuma tarukan mambobi domin tantance halin da yajin aikin ke ciki a faɗin ƙasar.

Haka kuma JOHESU ta mayar da martani kan wata sanarwa daga Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, wadda ta umurci shugabannin asibitoci da daraktocin gudanarwa su aiwatar da manufar “babu aiki babu albashi”.

Ƙungiyar ta bayyana manufar a matsayin wata dabara da gwamnati ke yawan amfani da ita domin matsa lamba kan ma’aikata, musamman idan ta jinkirta warware rikicin aiki.

JOHESU ta ce ta bi dukkan matakan da Dokar Rikicin Aiki ta tanada kafin fara yajin aikin, tare da jaddada cewa yajin aikin ya halatta bisa doka, ba karya ƙa’idojin hulɗar ma’aikata ba.

Ƙungiyar ta yi kira ga mambobinta da kada su karaya, tana mai neman su ci gaba da nuna haɗin kai da jajircewa, yayin da ta ce za ta ƙara sa ido, gudanar da tsare-tsare na matsin lamba da kuma amfani da kafofin yaɗa labarai domin cimma buƙatunta.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here