Kwankwaso ya zargi gwamnatin Kano da matsa lamba kan zaɓaɓɓun shugabanni da waɗanda aka naɗa kan su shiga APC

Dr. Rabiu Musa Kwankwaso 750x430

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Jihar Kano da tilasta wa shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli, sakatarori da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf su cika takardun nuna biyayya da shiga jam’iyyar APC, lamarin da ya haifar da tashin hankali da damuwa a faɗin jihar.

Kwankwaso, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya bayyana wannan zargi ne a wani faifan bidiyo da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ya wallafa a kafar Facebook.

A cikin bidiyon, ya yi bayani kan irin matsin lamba na zuciya da tunani da ke addabar mambobin NNPP sakamakon shirin sauya sheƙa zuwa APC.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta ƙirƙiri wani tsari da ke tilasta wa shugabannin ƙananan hukumomi da masu muƙaman siyasa fito-na-fito su bayyana wace ƙungiya suke mara wa baya tsakanin Kwankwasiyya da Gandujiyya, abin da ya sa mutane da dama suka shiga cikin fargaba da tashin hankali.

Kwankwaso ya nuna cewa wannan lamari ya jefa shugabanni da dama cikin matsanancin damuwa, inda wasu ba sa iya bacci, wasu suka rude, yayin da wasu ma aka kwantar da su a asibiti ana musu ƙarin ruwa saboda tsananin damuwar da suka shiga.

Ya ce halin da ake ciki ya tilasta masa yin shawarwari da dama domin rage wa waɗanda abin ya shafa nauyin da ke kansu, domin tsayawa kan matsaya mai tsauri a wannan lokaci zai iya ƙara tsananta halin da suke ciki.

Saboda haka aka yanke shawarar barin duk wanda aka matsa masa ya cika takardun da ake buƙata domin samun sauƙi.

Kwankwaso ya jaddada cewa wannan mataki bai da alaƙa da zaɓen 2027, yana mai cewa lokacin irin waɗannan lissafe-lissafe bai yi ba tukuna.

Ya nuna ƙwarin gwiwar cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage tashin hankali a Jihar Kano, musamman ga waɗanda ke fuskantar matsin lamba.

Ya kuma tuna da abubuwan da suka faru bayan sauyin siyasa na shekarar 2015, inda ya ce cin amanar da aka yi a wancan lokaci ta jefa magoya bayansu cikin wahala na tsawon shekaru.

Duk da haka, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da nasarorin gwamnatin Kwankwasiyya tare da fallasa ayyukan gwamnatin da ta gabata da suka kawo cikas ga ci gaban jihar.

Bidiyon ya haifar da ra’ayoyi mabambanta a faɗin Jihar Kano, inda magoya baya da masu suka ke fassara kalaman Kwankwaso ta hanyoyi daban-daban, a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan jita-jitar shirin gwamnan Kano na sauya sheƙa zuwa APC.

Bayanin edita:

Jaridar Solacebase na neman afuwar masu karatu kan kuskuren da aka yi a baya wajen fassarar wani faifan bidiyo na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya nuna cewa ya goyi bayan shirin sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC.

Mun yi kuskuren fahimtar bidiyon ne a Hausa, kuma muna nadamar hakan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here