Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa JAMB ta sanar da fara sayar da fom ɗin rajistar jarabawar shiga manyan makarantu ta UTME da kuma shirin Direct Entry domin daukar dalibai na shekarar karatu ta 2026 zuwa 2027.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na internet na X, inda magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya sanya hannu a kai.
Sanarwar ta nuna cewa jarabawar UTME ta shafi dukkan daliban da suka cika ka’idojin neman gurbin karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu a fadin Najeriya domin shekarar karatu ta 2026 zuwa 2027.
Hukumar ta ce rajistar UTME za ta fara ne a watan Janairu na 2026 kuma za ta rufe a watan Maris na 2026, yayin da za a gudanar da jarabawar UTME a watan Afrilu na shekarar 2026.
Ta kuma bayyana cewa rajistar UTME, har da na daliban da ke kasashen waje, za ta gudana daga ranar Litinin 26 ga Janairu zuwa Asabar 28 ga Fabrairu na 2026, tare da jaddada cewa dukkan masu nema dole ne su mallaki lambar tantancewa ta kasa NIN kafin su yi rajista.
Dangane da shekarun cancanta, hukumar ta ce galibi dole ne mai neman gurbin karatu ya kai akalla shekaru 16 kafin karshen watan Satumba na 2026, amma ta ce za a iya yi wa wadanda ba su kai shekarun ba rangwame bayan an tantance su sosai bisa sharudda na musamman.
Game da shirin Direct Entry, hukumar ta ce sayar da takardun nema da lambar E-PIN zai fara ne daga watan Maris zuwa watan Afrilu na 2026, kuma rajistar za ta gudana ne kawai a ofisoshin jihohi da yankuna na hukumar.
Ta kuma sanya lokacin jarabawar UTME daga tsakiya zuwa karshen watan Afrilu na 2026, tare da shirya jarabawar gwaji ta Mock UTME a karshen watan Maris.













































