Wata ƙungiya mai haɗakar kungiyoyin rashin ci gaban al’umma sama da 20 a ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin ci gaban al’umma na ta Kano ta jinjinawa Babbar Mai Shari’a ta Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, saboda irin jagorancin hangen nesa da ta nuna da kuma sauye-sauye masu zurfi da suka sake fasalta harkokin gudanar da shari’a a jihar.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Laraba a Kano, ta bayyana cewa Mai Shari’a Aboki ta nuna cikakkiyar sadaukarwa wajen inganta tsarin gudanarwa, gaskiya, da ɗorewar amana a cikin kotuna, tana mai bayyana lokacin shugabancinta a matsayin juyin juya hali a tarihin shari’ar jihar.
Tun bayan naɗinta a matsayin mace ta farko da ta zama Babbar Mai Shari’a ta Jihar Kano, ta jagoranci shirin gyaran fuska da ya ƙarfafa ’yancin kotuna, ya haɓaka amincewar jama’a, tare da inganta yadda ake gudanar da shari’a cikin sauri da inganci.
Ƙungiyar ta ce gyaran ginin kotuna da sabunta kayan aiki, musamman a Babban Kotun Jiha ta Kano, na daga cikin manyan nasarorin da ta cimma.
Wannan ya inganta yanayin aiki ga alkalai, lauyoyi, da jama’a, tare da samar da muhalli mai sauƙin shiga da ke karfafa adalci ga kowa da kowa.
Karanta: Kano: Mashahurin masanin tarihi da harkokin ilimi, Dakta Nasir Dantiye, ya rasu yana da shekaru 76
Haka kuma, ƙungiyar ta yabawa yadda ta tafiyar da harkokin kuɗi cikin gaskiya, inda ta bayyana cewa ofishin kula da tattara dukiya (sashen Probate) ya samu tara sama da naira miliyan 220 — abin da bai taɓa faruwa ba cikin shekaru fiye da talatin.
Wannan ya nuna tsantsar gaskiyarta da jajircewar ta wajen kare amana da dawo da kuɗaɗen da aka karkatar.
A ɓangaren jin daɗin ma’aikata, ƙungiyar ta bayyana cewa ta ƙara alawus ɗin man fetur na alkalai daga naira 120,000 zuwa naira 150,000, abin da ƙungiyar ta ce ya ƙarfafa gwiwar su.
Ta kuma kawo sauye-sauye ta hanyar zamani irin su tsarin shigar da ƙorafi ta yanar internet da adana bayanan kotu a kwamfuta, da horas da ma’aikata akai-akai, wanda hakan ke rage jinkirin shari’a da ƙara gaskiya.
Haka kuma, ƙungiyar ta yaba da yadda Mai Shari’a Aboki ta dawo da amincewar jama’a ga kotuna tare da ƙarfafa matsayi da rawar da mata ke takawa a shugabanci.
Ta ce kasancewar ta mace ta farko da ta hau wannan matsayi, alama ce ta ƙarfin hali, gaskiya, da jagoranci na garambawul.
A ƙarshe, ƙungiyar ta kira lauyoyi, masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin farar hula, abokan ci gaba, da jama’a gaba ɗaya da su ci gaba da marawa shirin gyaran tsarin shari’a baya domin tabbatar da dorewarsa.
Ta ce, harkokin shari’a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Dije Aboki ta kafa sabon mizani na ingantaccen shugabanci wanda ya kamata a yi koyi da shi a fadin ƙasa.












































