Tsohon ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Geoffrey Nnaji, ya bayyana cewa murabus dinsa daga majalisar ministocin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yayi ne ba saboda wani laifi ba, illa dai shawara tasa ta kashi ta kai.
Nnaji, wanda aka naɗa a watan Agustan shekara ta 2023, ya sanar da murabus dinsa ta cikin wata wasika da ya rubuta wa shugaban ƙasa a ranar Talata, inda ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi ta yin aiki a gwamnatin tarayya.
An tabbatar da wannan batu ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja, inda aka bayyana cewa murabus ɗin ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi masa na mallakar takardun karatu na bogi.
Labari mai alaƙa: Da ɗumi-ɗumi: Ministan kimiyya da fasaha ya sauka daga muƙamin sa
Ya bayyana cewa a cikin makonnin da suka gabata, wasu mutane sun kaddamar da binciken da ke neman bata masa suna ta siyasa da ƙarya a kafafen labarai na jaridu, rediyo, talabijin da kuma internet domin ɓata masa suna.
Tsohon ministan ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen marasa tushe sun jawo masa damuwa kuma sun shagaltar da shi daga gudanar da aikinsa yadda ya dace.
Ya ce ya shafe fiye da shekaru hamsin yana gina suna bisa gaskiya, aiki tukuru, da hidima ga al’umma.
Ya ƙara da cewa bai so waɗannan maganganun ƙarya su lalata kyakkyawar manufa da tsarin gaskiya da gwamnatin yanzu ke ƙoƙarin tabbatarwa ba, don haka ya yanke shawarar yin murabus domin bai wa doka damar yin aikinta yadda ya kamata.
Nnaji ya bayyana cewa murabus dinsa shawara ce ta kai tsaye domin mutunta tsarin doka da kare mutuncin shari’ar da ke gudana a kotu, yana mai nuna tabbacin cewa adalci zai tabbatar da gaskiya a ƙarshe.













































