Rashin zuwa makaranta: Kaduna za ta horar da jami’an kula da makarantu su 8,700

Screenshot
Screenshot

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta horas da mambobin kwamitin kula da makarantu 8,700 domin inganta ilimin boko a jihar.

Mukaddashin shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna (KADSUBEB) Mubarak Muhammad ne ya bayyana haka a wajen bude horon kwanaki shida na jami’an wayar da kan jama’a (SMOs) guda 92 a ranar Litinin a Kaduna.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa UNICEF ne ke tallafa wa horon tare da hadin gwiwar gwamnatin Kaduna da shirin tura yara Makarantu (ROOSC) da sauran hadin gwiwar masu rajin ci gaba.

Jami’an guda 92 sun fito daga kananan hukumomi 23 na jihar kuma za su zama manyan masu horarwa a fadin kananan hukumomin.

Muhammad ya kuma ce, horon zai mayar da hankali ne kan yadda za a sa yaran su koma makaranta, domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta dukufa wajen ganin ta rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda ya kara da cewa horon zai yi tasiri sosai a bangaren ilimi na asali.

Karin karatu: Kwalejojin ilimi a Najeriya za su fara ba da shaidar digiri

Shugaban riko na KADSUBEB ya kara jaddada kudirin gwamnatin jihar na bunkasa kwazon ‘yan kasa da kuma samar da kyakkyawar makoma ga matasan ta.

Jami’in ilimi na UNICEF, ofishin huy da ke Kaduna, Bala Dada, ya koka kan yadda jihar ke fuskantar matsalar kananan yara da ba sa zuwa makaranta.

Dada ya bayyana cewa, ta hanyar hadin gwiwa, UNICEF da sauran abokan hulda sun yi amfani da tsarin al’umma da tallafin gwamnati don magance matsalolin da ke haifar da rashin zuwa makaranta.

Wannan, a cewarsa, na iya zama sanadiyyar talauci, rashin tsaro ko rashin sani.

Shi kuwa Ko’odinetan aikin ROOSC, Mista Ezra Angal, ya ce horon wani shiri ne na saka hannun jari wajen gudanar da makarantu karkashin jagorancin al’umma.

Ya kara da cewa, kwamitin SBMC ya zama wata kafa ce tsakanin makarantu da al’ummomin da suke yi wa hidima, don tabbatar da cewa kowane yaro yana da hanyar samun ilimi mai inganci.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here