Bayan kammala digiri na farko, daliban jami’ar FUD tara sun sami tallafin cigaba da karatu a wata jami’a dake kasar chana, karkashin tsarin bada tallafin karatu da gwamnatin chana take bayarwa, mai taken (ANSO).
Jaridar Solacebase ta ruwaitu cewa daliban da suka sami tallafin karatun sun fito ne daga sashin Microbiology, Biotechnology da kuma Chemistry.
Shugaban sashin dake kula da harkokin dalibai, Farfesa Ahmed Muhammad Gumel, ya shaidawa Newsletter cewa dalibai biyu sun sami tallafin tun a shekarar 2021 sauran dalibai bakwai kuma sun sami tallafin a shekarar 2022.
Ya kara da cewa dalibai 34 ne kadai daga jami’o’in Najeriya suka sami tallafin karatun na gwamnatin ta chana a shekarar 2022.
A nasa bangaren, shugaban jami’ar ta FUD ya taya daliban murna bisa samun tallafin karatun, ya kuma yaba musu bisa daga sunan jami’ar ta FUD da suka yi.













































