Minstan sifiri Alhaji Mu’azu Sambo, ya yi barazanar dakatar da Kamfanin ‘yan chana na (CCECC), dake aikin titin jirgin kasan Kano zuwa Kaduna da kuma Maiduguri zuwa port Harcourt, bisa gazawar Kamfanin na kamala kaso 85 na aikin kamar yacce aka tsara.
Ministan ya bayyana hakan ne ya yin ziyyar gani da ido da ya kai tashar ruwa ta Lekki a jihar Lagos ranar Asabar.
” Har yanzu Kamfanin CCECC, bai kammala kason da muke da bukata ya yi ba, amma na basu nan da 30 Oct. Idon har basu kammala ba nasan matakin da zan shawarci shugaban kasa ya dauka akan su.” Injishi.
Ya kuma bayyana gamsuwar da yacce aikin tashar ruwa ta Lekki yake tafiya.
NAN













































