TUC ta soki yunkurin siyar da asibitoci mallakin gwamnatin tarayya

Trade Union Congress
Trade Union Congress

Kungiyar TUC ta soki yunkurin da gwamnati ta ke yi na siyar da asibitoci mallakin gwanatin tarayya a fadin kasa baki daya.

Shugaban kungiyar, Mista Festus Osifo, ne ya shaidawa manema labarai haka a Abuja, ranar juma’a, jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da kungiyar tayi.
Ya ce talakawa basu taba amfana da siyar da kadarorin gwamnati da aka yi a baya ba, kuma yanzu ma haka baza su amfana da komai ba, saboda haka TUC ita ma bata goyan bayan hakan.
“ Babu wani abu da talaka ya amfana dashi a irin siyar da kadarorin gwamnati da aka yi a baya, kamar siyar da bangaren wutar lantarki da akayi mai talaka ya amfana da shi” Injishi.
Ya yin da yake magana akan yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dinga girmama harkokin ilimi a kasar nan.
“TUC zata yi kokari don ganin an cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU da kuma gwamnatin tarayya.”
A ya yin zan tawar ta sa da manema labarai, ya kuma soki siyawa Niger motoci na kimanin 1.4 biliyan, da gwamantin tarayyar tayi, inda ya ce hakan sam bai da ce ba, a irin wannan hali na matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan.
Sannan kuma shugaban na TUC ya yi kira ga gwamnatin da tayi duk mai yuwuwa don magance matsalar tsaro da ta’addanci da suka addabi kasar nan.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here