Aiwatar da Sabbin Manhajoji Na Jami’o’i Zai Fara Daga Satumba 2023 – NUC

National Universities Commision NUC
National Universities Commision NUC

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta ce za a fara aiwatar da tsarin koyar da karatu mafi kankanta na (CCMAS) nan da Satumbar 2023.

Ana sa ran CCMAS za ta jagoranci wajen tsara manhajoji don shirye-shiryensu tare da kawo sabbin abubuwan da suka dace domin bunkasa ilimi a fadin kasa baki daya.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki kan CCMAS a Abuja ranar Laraba, Mukaddashin Sakataren Hukumar NUC, Chris Maiyaki ya ce tsarin zai  mayar da jami’o’in Najeri suyi fice a Afirka.

A cewarsa, aiwatar da aikin zai taimaka wajen kara kaimi ga fannin ilimi a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here