Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta fara horar da mata guda 30 na tsawon mako biyar kan gyaran wayar salula a jihar Kano.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa horon wanda aka fara a ranar Litinin ya hada da dattijai da ‘yan mata daga sassa daban-daban na jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, babban Daraktan CITAD, Dakta Y Z Ya’u, wanda Muhammad Bello Yahaya ya wakilta, ya ce sun gudanar da horon ne da nufin wadata mata da sana’o’in gyaran wayar hannu domin su kasance masu dogaro da kai.
“A karshen horon, za mu ba su kayan aikin gyaran wayar domin su kasance masu dogaro da kansu kuma su kasance masu daukar ma’aikata suma.”
A nata bangaren, Harira Wakili, wacce ta gabatar da makala a wajan taron, ta ce akwai bukatar a horas da mata kan gyaran waya, ta yadda za su zama masu samar da ayyukan yi a tsakanin al’ummominsu.
Wakili ta jaddada rawar da fasahar sadarwa ta ke takawa wajen karfafawa mata gwaiwa, ta kuma bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da zasu koya ya yin horon.