Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce an kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba su 21 da suka hada da wani shugaban al’umma da wasu ‘yan kasar China 3 a kauyen Azam da ke kusa da jihar Nasarawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh ta fitar.
Ta ce aikin da ya kai ga cafke wanda ake zargin, mai suna: “Safe G-7” ya biyo bayan mummunar barazanar garkuwa da mutane da ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka a cikin Abuja da jihohin da ke makwabtaka da ita.
Adeh ta ce shugabannin jami’an tsaro a yankin sun kai wani gagarumin farmaki tare da tsaftace su a duk maboyar da aka yi taswirori, sansanonin da kuma wuraren da suka zama mafaka ga barayin.
Ta ce an kai harin ne da nufin magance matsalar garkuwa da mutane da ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka a cikin jihohi bakwai da suka hada da Kogi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Benue, Plateau da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A cewarta, ci gaba da aikin da aka yi a ranar Talata a Matte, karamar hukumar Kwali, domin kwato kauyen da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka mamaye, ya yi nasara kuma nan take aka tura sojoji domin samar da tsaro da ake bukata.
Adeh ta ce akasarin wadanda ake zargin sun fito ne daga jihohin da ke kan iyaka, kuma sun samu hadin kai ba tare da wani bata lokaci ba da shugaban al’ummar yankin wanda nan take aka kama su.
DSP Josephine Adeh ta ce za a mika wadanda ake zargin biyu da ke da alaka da mallakar magungunan da aka ambata ga hukumar NDLEA, inda ta bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.













































