Satar Jarabawa: Wata kwaleji a Kano ta kori dalibai 12

00AA1F24 B8B5 480D B63F 3EA307EB493D
00AA1F24 B8B5 480D B63F 3EA307EB493D

Kwalejin Kimiyya da Fasahar lafiya ta Aminu Dabo dake Kano ta kori dalibai 12, bisa samun su da laifin satar amsa a lokacin da suke rubuta jarabawa.

Wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na kwaleji, Abdullahi Usman ya fitar a ranar Talata, ta ce an kama wasu dalibai 13 (‘yan aji 2) bisa laifuka daban-daban da suka shafi rashin da’a a yayin gudanar da jarrabawa a makarantar.

Sanarwar ta ce an kama  daliban suna tafka magudin jarrabawa da rashin da’a da ya saba wa ka’ida da ka’idojin Kwalejin a lokacin jarrabawar zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Sanarwar ta ce, ”Hukumar Kwalejin ta dauki mataki  kan daliban ne Saboda abin da  suka yi ya saba da dokar makarantar, inda aka yi amfani da shawarwarin da kwamitin ladabtarwa ya bayar.

“Rahotanni sun nuna cewa daliban da abin ya shafa an kama su da hannu dumu-dumu cikin rashin da’a da kuma wasu abubuwa da suka saba wa tsarin kwalejin a lokacin jarrabawar zango na biyu na 2021/2020.

Hukumar gudanarwar, ta umurci sauran daliban da aka wanke da su koma kwalejin a ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, 2022 domin ci gaba da jarrabawa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Haka zalika ya gargadi daliban da abin ya shafa da su kaurace wa harabar kwalejin domin gujewa duk wata shari’a.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here