Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta umurci Gwamnatin Jihar Kano da ta dawo da wani shaida da ake tuhuma don sake sake amsa tambayoyi dangane shari’ar da ake yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara.
NAN ta ruwaito cewa ana tuhumar Nasiru-Kabara da laifuffuka guda hudu da suka hada da kalaman batanci ga Annabi Muhammad, wanda ya aikata a ranar 10 ga watan Oktoba, 25 da kuma Dec.20, 2019.
Ana zargin wanda ake tuhumar da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a aurensa da Nana Safiyya a cikin Jautul Fara, sashi na 93 (40) da hadisi na 1,365 da 1,428.
Lauyan wanda ake, Ambali Obomeileh-Muhammad, SAN, ya bukaci kotun da ta dawo da shaida na farko domin sake yi masa tambayoyi bisa tanadin sashe na 36 (5) 6 (a) (b) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Lauyan masu gabatar da kara, Suraj Sa’eda SAN, ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar inda ya kara da cewa masu kariya ba su bayar da dalilan da ya sa za’a dawo da shaidar ba.
Alkalin kotun, Malam Ibrahim Sarki-Yola, bayan ya saurari dukkan bangarorin biyu ya amince da bukatar sannan kuma ya umarci lauyan masu shigar da kara da ya dawo da shaida na farko domin sake yi masa tambayoyi.
Ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu, domin sake yin jarrabawar.