A karshe Shugabancin riko na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC takarda, inda ta sanar da ita babban taronta na kasa da za ta gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairu.
An dai yi ta rade-radin cewa wasu ‘yan siyasa a cikin jam’iyyar na shirin sauya ranae babban taron.
Sai dai a cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Fabrairu mai dauke da sa hannun Gwamna Mai Mala Buni da Sakatare, Sanata John James Akpanudoedehe, jam’iyyar ta ce za ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar.