Inuwa Waya ya nuna damuwa kan karuwar ayyukan daba a Kano, ya yi kira da a inganta harkar ilimi

WhatsApp Image 2025 06 11 at 10.36.24 750x430 (1)

 

Malam Inuwa Waya, daya daga cikin wandanda suka nemi takarar gwamna a APC a 2023, ya bayyana damuwa kan yadda ‘yan siyasa ke amfani da matasa a matsayin ‘yan daba, suna ba su miyagun kwayoyi da alkawuran karya don tayar da hankali.

Waya ya bayyana hakanne a wani jawabi da ya gabatar ga manema labarai jiya a Kano.

Waya ya ce wannan matsala ta samo asali daga yawan yara marasa zuwa makaranta a jihar, inda ya bayyana cewa sama da yara miliyan daya basu zuwa makaranta.

Ya kuma kara da cewa wannan yasa suke shan kwayoyi da karbar kudi don yin barna a siyasa.

Ya koka kan yadda gwamnatocin da aka yi a jihar da gazawa wajen bayar da horo ga malamai da gyara makarantu.

Waya ya tuna lokacin da makarantu a Kano suka kasance na zamani, suna da malamai ‘yan kasashen waje, kayan karatu kyauta, da horarwa ta musamman.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gyara fannin ilimi ta hanyar: gyara makarantu, daukar malamai kwararru, bunkasa sana’o’i, da bayar da tallafi ga dalibai.

Ya gargadi cewa rashin daukar mataki na gaggawa kan iya jefa jihar cikin mawuyacin hali nan gaba.

Ya kuma jaddada muhimmancin bayar da tallafin karatu na kasashen waje a fannonin da ba a iya samu a cikin gida Najeriya, tare da kuma karfafawa dalibai masu hazaka gwiwa.

Haka kuma Waya ya yi kira da a farfado da shirye-shiryen samar da ilimin bai daya.

Ya kara da cewa in har ba a zuba hannun jari a cikin harkokin matasa da tsarin ilimi na Kano ba, akwai hadarin rasa makomar jihar saboda talauci, tashin hankali, da rashin kyakkyawan shugabanci.

Ya kuma shawarci gamnatoci da su inganta harkar ilimi ta hanyar daukar kwararrun malamai da kuma biyansu albashin da zai ishesu gudanar da rayuwarsu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here