Kotun Daukaka Kara dake Abuja ta yi watsi da wasu bukatu guda biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar a kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.
A hukuncin da wani kwamitin alkalan kotun ya yanke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, kotun ta watsar da bukatun ne bayan lauyoyin Akpabio sun janye su.
Lauyoyin Akpabio sun nemi lokaci domin daukaka kara kan hukuncin da wata kotun tarayya ta yanke a Abuja a ranar 10 ga Maris, 2025, inda Natasha ta shigar da kara kan wasu shugabanni na Majalisar Dattawa. Amma kotun ta ki amincewa da bukatunsa.













































