Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano wasu mutane 96 masu taimakawa ta’addanci a fadin kasar nan ta hanyar bawa ‘yan ta’adda kudi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin ke yi a Abuja a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu.
Ya ce, “Sashin kula da harkokin kudi na Najeriya (NFIU), a shekarar 2020-2021, ya gano masu kudi 96 dake taimakawa ta’addanci a Najeriya,” yayin da mutane 424 ke hulda ta kudi da ‘yan tada kayar baya na kungiyoyin Boko Haram da Iswaf.
Har ila yau, kimanin kamfanoni 123 da da masu canjin kudade kimanin 33 aka gano suna da alaka da ‘yan ta’adda baya ga wasu mutane 26 da ake zargin ‘yan fashi da garkuwa da mutane ne da kuma wasu 7 da aka gano a yanzu.
A daidai wannan lokacin, 2020-2021, kungiyar ta mayar da kudaden da aka samu ta hanyar zamba da suka kai dalar Amurka $103,722,102.83, 3,000 Pound Sterling; Dalar Singapore 7,695, da Yuro 1,091 ga kasashe 11 da abin ya shafa da suka shigo kasar.













































