Amurka ta nuna damuwa kan dokar hana neman jinsi a Ghana

Amurka, Ghana, doka, jinsi, nema, damuwa
Amurka ta ce ta damu matuƙa da yadda Ghana ta amince da ƙudurin dokar hana neman jinsi abin da ta ce na barazana ga 'ƴancin tsarin mulki. "Ƙudurin zai kuma...

Amurka ta ce ta damu matuƙa da yadda Ghana ta amince da ƙudurin dokar hana neman jinsi abin da ta ce na barazana ga ‘ƴancin tsarin mulki.

“Ƙudurin zai kuma lalata tsarin lafiyar al’umma na Ghana da kafofin yaɗa labarai da tattalin arziki,” in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller, cikin wata sanarwa.

Amurka dai ta nemi a sake nazarin matsayin ƙudurin a kundin tsarin mulki.

Karin labari: “Likitoci na iya fuskantar matakin shari’a” – Gwamnatin Koriya ta Kudu

Sabon kudurin dokar da aka amince da shi ranar Laraba ya tanadi hukuncin shekara kusan uku a gidan yari ga duk wanda yake nuna kansa a matsayin mai neman jinsi.

Ya kuma tanadi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar ga wanda ya kafa ƙungiyar neman jinsi ko ɗaukan nauyin masu aƙidar.

Ƙungiyoyin kare ‘ƴancin bil-adama sun caccaki matakin amincewa da ƙudurin dokar.

Ƙungiyar Rightify Ghana ta yi kakkausar suka kan matakin wanda a cewarsu ke zama barazanar mutuwa ga ‘ƴancin masu neman jinsi a ƙasar”.

Karin labari: Kamfanin MTN ya bayyana dalilan katsewar sadarwa

Shugabar hukumar UNAIDS mai yaƙi da cutar ta HIV Aids ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, Winnie Byanyima ta ce idan ya zama doka, yana iya janyo hatsaniya a tsakanin ‘ƴan Ghana.

Za’a gabatar da ƙudurin dokar ga shugaba Nana Akufo Addo inda yake da mako ɗaya ya sanar da shugaban majalisa kan ko ya amince da ƙudurin ko kuma a’a, kamar yadda kundin tsarin mulkin Ghana ya tanada.

Idan kuma ya ƙi sa hannu, yana da kwana 14 ya bayar da dalilan da ya sa yake ganin ya kamata majalisa ta sake nazari a kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here