Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta mayar da naira biliyan 4.4 ga Hukumar Jin Dadin Alhazai na jihohi 36, Babban Birnin Tarayya (FCT), da Sojoji, biyo bayan matsalolin da suka faru yayin aikin Hajjin 2023.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis a Abuja, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na NAHCON, Malam Muhammad Musa, ya bayyana cewa kudin da aka mayar ya shafi hidimar wutar lantarki da ba a gudanar yadda ya kamata ba a lokacin Masha’ir (tsakanin aikin Hajji) daga bangaren hukumomin Saudiyya.
Haka nan, NAHCON ta mayar da naira miliyan 917.1 ga kamfanonin jigilar alhazai 192 da aka tantance, tare da umarnin raba kudaden ga maniyyatansu. Za a ci gaba da biyan sauran kamfanonin da suka halarta bayan daidaita abubuwan da suka rage.
“Wannan mayar da kudin yana nuna jajircewar Hukumar wajen yin aiki cikin gaskiya da rikon amana karkashin jagorancin Shugabanta, Farfesa Abdullahi Saleh Usman,” inji Musa.
Ya shawarci dukkan maniyyatan da suka halarci aikin Hajjin 2023 da su tuntuɓi Hukumar Jin Dadin Alhazansu ta Jihohi ko kamfanonin jigilar alhazai don karɓar kuɗaɗensu, inda kowanne mahajjaci ke da hakkin karɓar N61,080.
Dangane da aikin Hajjin 2025, NAHCON ta yi kira ga maniyyatan da ke shirin zuwa su biya kudin Hajji da wuri domin samun damar shirya komai cikin lokaci daidai da ka’idojin da Saudiyya ta gindaya.
Domin tabbatar da gaskiya a cikin aikin, hukumar ta nemi Hukumar EFCC, ICPC, da sauran hukumomin tsaro su sa ido sosai a kan rabon kudaden.
“Wannan hadin gwiwar zai taimaka wajen tabbatar da cewa kudaden sun isa ga wadanda aka yi niyya ba tare da wata matsala ba,” in ji Musa.