Zan ci zabe na ko da babu Peter Obi a jam’iyyar Labour – Alex Otti

IMG 20230324 WA0012
IMG 20230324 WA0012

Alex Otti, zababben gwamnan jihar Abia, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar Labour ne kafin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi ya koma, inda ya kara da cewa da ya ci zabe ba tare da shi a jam’iyyar ba.

Mista Otti yayi kurin cewa ya taba lashe zaben gwamna ba tare da Peter Obi ba.

Otti, wanda ya yi magana a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels, ya dage cewa shi ne ya lashe zaben 2015 wanda ya samar da Okezie Ikpazu a matsayin gwamna a karkashin jam’iyyar APGA.

An ayyana Otti a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar 18 ga Maris a ranar Laraba. Ya kuma bayyana cewa ya koma jam’iyyar Labour ne kafin Peter Obi.

Ya ce, “A shekarar 2015 da na yi takara a karkashin jam’iyyar APGA, babu Peter Obi. Kuma kuna da labarin cewa ni na ci zaben. A lokacin da muka shiga jam’iyyar Labour, Peter Obi bai shiga ba.

“Sai kusan mako guda kafin ya kira ni ya ce ya sayi fom din takarar shugaban kasa kuma yakan ziyarci jihad domin kamfe cikin jamiyyar Labour,” in ji shi.

Sai dai Otti ya amince da tsohon gwamnan Anambra kan tasirin da ya yi a zaben da aka kammala, inda ya ce Obi “ya zo Abia kusan sau hudu domin ya yi mana yakin neman zabe.

“Peter Obi wani babban jigo ne a yakin neman zabenmu, amma zan iya fada muku cewa mun ci zabe a baya a Abia ba tare da shi ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here