Kano ta fara shirin samar da babban tsarin samar da ruwan sha na shekaru 20 – Hukuma

Facebook 1794893183837 7528327660543740255 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta fara samar da cikakken babban tsarin samarwa da rarraba ruwan sha na tsawon shekaru 20, domin tabbatar da dorewar samun tsaftataccen ruwan sha a birane da yankunan karkara.

SolaceBase ta rawaito cewa Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar, Dr Dahiru M. Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan da ma’aikatar ta gudanar da taron farko na fara aikin samar da wannan dogon tsari.

Hashim ya bayyana shirin a matsayin wani babban abin tarihi, inda ya ce wannan ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan shiri na dogon lokaci a tarihin Kano, na farko ya kasance a zamanin mulkin marigayi Gwamna Audu Bako.

Kwamishinan ya ce, “Wannan shiri ne mai cike da tarihi ya nuna hangen nesan Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf na gina ingantaccen bangaren samar da ruwa wanda zai iya biyan bukatun al’umma mai saurin karuwa har tsawon shekaru masu zuwa.”

Ya bayyana cewa babban tsarin ba wai takardar manufofi ba ce kawai, wani tsari ne na aiki da zai tabbatar da dorewar tace ruwa, fadada hanyoyin rarraba shi da kuma samar da ingantaccen ruwan sha ga al’ummar jihar.

A cewarsa, ma’aikatar za ta hada gwiwa da kwararru a fannin, abokan huldar ci gaba da shugabannin al’umma wajen tsara wannan shiri, domin tabbatar da cewa ya dace da bukatun jihar tare da samar da zuba jari na zahiri a bangaren ruwa.

“A mataki na gaba, za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kwararru a fannin, abokan huldar ci gaba da shugabannin al’umma domin tabbatar da cewa wannan shiri na shekaru 20 ya haifar da zuba jari mai dorewa da kuma samar da ruwan sha ba tare da katsewa ba ga al’ummar yanzu da kuma masu zuwa nan gaba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here