Bauchi: Tsohon ɗan takarar gwamnan NDC ya koma APC

Bauchi NDC Gov

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Ibrahim Muhammad Kashim, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Kashim ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam’iyyar APC yayin wani bikin karɓarsa a hukumance da aka gudanar a ranar Litinin a Bauchi.

Ya ce ya koma APC ne saboda jam’iyyar ce ke da babbar damar bai wa Jihar Bauchi damar taka muhimmiyar rawa a harkokin mulki da ci gaban ƙasa.

A cewarsa, “A halin yanzu APC ce jam’iyya mai mulki a matakin tarayya, kuma tana da gagarumin rinjaye a faɗin Arewacin Najeriya. Haka kuma, ita ce jam’iyyar da ke da tsarin siyasa, yaɗuwar ƙasa baki ɗaya da ƙarfin hukumomi da za su samar da ingantaccen dandali na cimma muradun siyasa da ci gaban da muke son samu ga Bauchi.

“Na yi imanin cewa dole ne a sanya Bauchi a matsayi mai muhimmanci bisa wannan yanayin siyasa. Ba za mu iya yin caca da makomar jiharmu ta hanyar jingina burin ci gabanta ga wata jam’iyya da ba ta da irin wannan yaɗuwa da tasiri a matakin ƙasa ba.

“Dole ne muradun al’ummar Bauchi su zama jagorar duk wata shawara da za mu yanke, ba son rai, tsohon tarihin siyasa ko kuma sauƙin da wasu mutane za su samu ba.

“Bari in bayyana da farko cewa wannan mataki ba wai saboda takaici, son biyan buƙatar kai ko neman mukamin siyasa ba ne. Shawara ce da muka yanke bayan zurfafa tunani kan makomar siyasa da ci gaban Jihar Bauchi, tare da imanin cewa dole ne mu zaɓi abin da zai amfani al’ummarmu baki ɗaya.

“Lokacin da na fice daga jam’iyyar NDC a ranar 16 ga Oktoban 2026, na bayyana cewa tafiyar siyasar mu ba ta ƙare ba. Na kuma tabbatar wa magoya bayana cewa ƙudurinmu na ceto da bunƙasa Jihar Bauchi bai sauya ba. Wannan ƙuduri kuwa yana nan daram.
Ya ƙara da cewa siyasa tana ƙunshe da zaɓi, sauyin yanayi da kuma ci gaba da neman hanya mafi inganci wajen cimma muradun al’umma baki ɗaya.

“Yanzu mun zaɓi ci gaba da neman cikar wannan buri ne ta hanyar wani dandali da, bisa nazarinmu zai bai wa Bauchi babbar dama ta fuskar dabarun siyasa.”

Kashim ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NDC ne a wata wasiƙa da ya aika wa shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Bauchi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here