Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da shugaban ma’aikata na rikon kwarya kuma babban sakataren hukumar Salisu Mustapha, bisa zargin zarge-zargen da ake yi masa na zaftarewa ma’aikata albashi da kuma rashin biyan wasu ma’aikan albashinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa an kuma umurci Salisu Mustapha da ya ajiye mukaminsa na babban Sakatare a karkashin ofishin shugaban ma’aikata, don ba da damar gudanar da bincike ba tare da tangarda ba.
A cewar sanarwar, hwamnan ya amince da nadin Malam Umar Muhammad Jalo, babban sakataren REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riko, har sai an kammala binciken da ake yiwa dakataccen sakataren rikon kwarya.
Labari mai alaƙa: Gwamnan Kano ya ba da umarnin yin bincike kan batun zaftare albashin ma’aikata
Gwamna Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na daukan mataki kan duk wanda aka kama da laifin zartarewa ma’aikata kudi, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan sakamako.
SolaceBase ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin tare da yin kakkausan gargadi kan yadda wasu ma’aikatan ke kukan zaftare musu albashi da kuma rashin biyan albashin ga wasu ma’aikatan jihar tun watan Oktoban 2024.
Daga nan ne gwamnan ya kaddamar da kwamitin mutum bakwai da zai binciki lamarin, wanda Abdulkadir Abdussalam ke jagoranta, har ma ya bada wa’adin kwanaki bakwai don gano tushen matsalar da kuma gabatar da sakamakon binciken.
A farkon wannan watan ne aka nada Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riko, biyo bayan hutun jinya da aka baiwa babban shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya.