Wata kungiya mai zaman kanta, Save The Children International da GlaxoSmithKline ta karkashin shirin INSPRING ta fadada ayyukanta zuwa sama da manyan asibitoci hudu a jihar Jigawa.
Shugaban shirin INSPIRING, Dakta Adamu Isah ne ya sanar da fadada aikin a lokacin da yake mika iskar oxygen ta kudi naira miliyan 55 ga ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, wanda aka gudanar a ofishin kungiyar Save the Children dake Dutse.
A cewarsa, farashin iskar oxygen ya kai Naira miliyan 47 yayin da horar da likitoci, ma’aikatan jinya da kuma kwararrun likitocin halittu zai ci Naira miliyan 8.
Ya bayyana cewa, ofishin na jiha ya gabatar da bukatar bukatar fadada ayyukansu daga asibitocin gwaji (Kiyawa da Rasheed Shikoni Dutse) zuwa dukkan manyan asibitocin jihar.
Dokta Isah Adamu ya ci gaba da cewa, karin asibitocin guda hudu sun hada da manyan asibitocin Hadeja, Gumel, Babura da kuma Kazaure a jihar.
A nasa jawabin bayan karbar na’urorin iskar oxygen, babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa Dr Salisu Muaz, wanda ya samu wakilcin daraktan kula da asibitoci Dr Bashir Ahmed ya yabawa hukumar GSK/SCI bisa wannan tallafin.
Ya ba da tabbacin yin amfani da kayayyakin da aka bayar da su yadda ya kamata, ya kara da cewa, gwamnatin jihar Jigawa za ta ci gaba da hada hannu da shirin INPIRING domin inganta harkar lafiya.













































