Da DUMI-DUMI: Kotun koli ta ce umarnin da Buhari ya kan samar da kudaden ‘yan majalisar jihiho da bangaren shari’a ya sabawa kundin tsarin mulki

D2161DCA FDAA 4A1E AE24 F13FD2FA71B4
D2161DCA FDAA 4A1E AE24 F13FD2FA71B4

Kotun koli ta bayyana dokar ta 10 (EO10) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar game da samar da kudi ga bangaren shari’a da majalisar dokokin Jiha a matsayin haramtacce kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

A hukuncin da aka aka yanke ranar Juma’a, da yawa daga cikin alkalai 7  na kotun sun amince cewa shugaban ya zarce ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen bayar da EO10.

Dukkan alkalan 7 sun amince cewa Jihohin ba su da ikon a mayar musu da duk abin da suka kashe a baya don kula da wadancan kotunan.

Hukuncin ya kasance ne a kan karar da Jihohi 36 suka shigar da gwamnatin tarayya kan kudade na bangaren shari’a da kuma tsarin mulki na EO10.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here