Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci kasashe masu tasowa da su hada kai tare da karfafa dangantakarsu domin bunkasar tattalin arziki da kasuwanci a nahiyar.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Sarkin ya yi wannan jawabi ne a wani taro da kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu da noma ta Kano da ‘yan kasuwar Gambia suka yi a birnin Banjul na kasar Gambia a ranar Asabar.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, ”Dole ne mu yi duk abin da ya kamata don bunkasa hadin gwiwar wannan nahiya, musamman a yankinmu na yammacin Afirka”.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Sarkin ta fitar, inda ta ce Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa, ka’idoji daban-daban da ke cikin kungiyar ECOWAS sun ba mu tsarin hadin gwiwa wanda za a iya amfani da su domin amfanin kasashen gaba daya.
“Sarkin ya kuma bukaci mahalarta taron da su duba na tsanaki tare da binciko hanyoyin da za a samar da alakar da za ta amfanar da juna da za ta iya bunkasa tattalin arzikinmu. Ya bayyana cewa hakan na iya samar da damammaki da za su iya samar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ga al’ummominmu biyu da kuma fa’idar jama’armu baki daya,” in ji sanarwar.
Daga nan sai ya bukace su da su dage da kuma himma wajen kulla huldar kasuwanci mai dorewa.
A cewar sanarwar, Sarkin ya gode wa hukumomin Gambia da duk wadanda suka yi aiki tukuru, ciki har da babban kwamishinan, Ambasada Muhammad Manu bisa hangen nesa da goyon bayansu ga wannan taro.













































