Gwamnatin tarayya ta ce a shirye ta ke ta sanya na’ura sadarwa wadda ke bada hanya a yayin saukar jirgi mai suna Instrument Landing System (ISL) 3, a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano da filin jirgin sama na Fatakwal da kuma filin jirgin Katsina.
Mista Mathew Pwajok, Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA), ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja, lokacin da yake bayani ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Pwajok ya ce matakin zai kara yawan filayen tashi da saukar jiragen sama da ke da rukuni na 3 ISL a kasar zuwa biyar.
A cewarsa, tsarin saukar kayan aiki kayan ne na kewayawa da zama jagora ga jiragen sama a lokacin da suke sauka a filin jirgi ga jirgin sama, da kuma lokacin da zai tashi.
Shugaban NAMA ya bayyana cewa filin jirgin da ke Lafiya a Jihar Nasarawa, wanda kuma ke da rukunin 2 ILS ba a bude shi ba saboda har yanzu ba a fara aiki ba.
Pwajok ya ce har yanzu ana amfani da kayan aikin Categroy1 a wasu filayen jirgin sama, yana mai nuni da cewa gwamnati ta yi shirin maye gurbinsu da Mataki na 2 ILS.
“Muna da wasu na’urorin da za su iya jagorantar jiragen sama zuwa filayen saukar jiragen sama kuma muna kiran su da suna Very High Frequency Omni-Directional Range (VOR), tsarin lantarki na ƙasa wanda ke ba da bayanai ga manyan hanyoyi masu tsayi da ƙasa da hanyoyin filin jirgin sama.













































