Rundunar sojojin saman Najerya ta karyata wani labarin fara daukar ma’aikata da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta.
Hakan na dauke cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Edward Gabkwet, ya fitar ranar Litinin a Abuja, inda yake jawa mutane kunne da kar su fada hannun yan damfara.
Ya ce sanarwar daukar aikin ba daga garesu take ba, sanan kuma ya tunawa yan Najeriya cewa rundunar ta rega ta dau ma’aikata tun a baya.
Ya kara da cewa idan lokacin daukar ma’aikata yazo rundunar zata bi duk hanyar data dace domin sanar da mutane.