Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya roki gwamnatin tarayya data sake duba karin kudin makaranta da tai a makarantun kasar nan.
Ya roki gwamnatin data yi hakan domin samin shugabanni masu inganci a nan gaba
Osodeke yana magana ne domin kalubalantar karin kudin makaranta da gwamnatin tarayya tayi a makarantun sakandare mallakinta, da kuma karin kudin makaranta da akai a manyan makarantun kasar nan.
Ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ranar Lahadi a Lagos cewa karin kudin makarantar barazana ne ga ya yan talakawa da suke karatu a kasar nan.
Idon za’a iya tunawa dai jami’ar lagos na daya daga cikin wadan da suka kara kudin makaranta a kasar nan, daga Naira N25,000 zuwa N200,000, ya dan ganta da kos din da dalibi zai karanta.












































