Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barista Haruna Dederi ya ce hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar ya kore duk wani umarni da kotun tarayya ta bayar tare da kuma shata layi kan batun masarautar.
Dederi ya kuma nemi dukkanin masu hannu a rikicin su bi umarnin don ɗorewar zaman lafiya.