Kasar China za ta yafe bashin da ta ke bin Kasashen Afirka 17

China President 750x430 1
China President 750x430 1

Gwamnatin kasar China ta bayyana shirin ta na yafe wasu basukan kudi marasa ruwa guda 23 ga kasashen Afirka 17.

Kasar Chinan ta kuma bayyana aniyar ta na ba da taimakon abinci ga al’ummomin da ke fafutukar yadda zasu rayu.

Ministan harkokin wajen Kasar China Wang Yin ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Kasar China da Afirka wanda aka gudanar a baya-bayan nan, inda ya bayyana cewa matakin ya nuna aniyar kasar China na kara karfafa dangantakar tattalin arziki da nahiyar Afirka.

Sai dai ministan ya ki bayyana kasashen da ake bi bashin ko adadin rancen.

Wani bangare na jawabin ya kuma ce, kasar ta China za ta fadada shigo da kayayyaki daga Afirka.

“Za kuma mu ci gaba da kara yawan shigo da kayayyaki daga Afirka, da tallafawa bunkasar ayyukan noma da masana’antu na Afirka, da fadada hadin gwiwa a masana’antu masu tasowa” in ji sanarwar.

Kazalika, bisa kudurin da ta yi na yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, China ta ce za ta sake tura dala biliyan 10 zuwa Afirka ta karkashin asusun bada lamuni na duniya IMF.

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here