Naira ta karu a kasuwar canjin kudade

naira, dala, farashi, karu, canjin kudade
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Naira ta kara daraja zuwa 1,350 kan kowacce dala a kasuwar dala daga Naira 1,370 a makon jiya. Hakazalika, darajar...

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Naira ta kara daraja zuwa 1,350 kan kowacce dala a kasuwar dala daga Naira 1,370 a makon jiya. Hakazalika, darajar Naira ta ragu zuwa 925.34 kan kowacce dala a kasuwar canjin kudi ta Najeriya NAFEM.

Karanta wannan: Iyalan marigayi Akeredolu sun sanar da ranar Jana’izarsa

Bayanai daga FMDQ sun nuna cewa farashin canjin NAFEM ya tashi zuwa Naira 925.34 akan kowace dala daga 902.45 a karshen makon da ya gabata, wanda hakan ke nuna faduwar darajar Naira 22.89.

Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin farashin canji na hukuma da na kasuwa ya ragu zuwa Naira 397.92 a kowace dala ranar Litinin daga 467.55 kowace dala a karshen makon da ya gabata.

Karanta wannan: Amurka da Burtaniya sun kara kai hari kan mayakan Houthi

Adadin dala da aka yi ciniki ya fadi da kashi 12 cikin 100 zuwa dala miliyan 565.82 a makon jiya daga dala miliyan 645.97 na baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here